Sports
Real Madrid ta sayo Dan wasan da zai maye gurbin Benzema
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Real Madrid ta kulla kwantiragi da dan wasan Sifaniya, Joselu daga Espanyol akan aro cikin tsawon kaka, amma yarjejeniyar ta bada damar sayen sa a karshen kakar.
Joselu mai shekaru 33, shi ne na uku a jerin ‘yan wasan da suka fi zura kwallaye a gasar La Liga ta kakar da ta gabata, inda ya zura kwallaye 16 a raga duk kuwa da cewa, kungiyarsa ta tsunduma ajin ‘yan dagaji.
Zamu Tabbatar Da Jagoranci Na Gari, Ba Tare Da Son Zuciya Ba – Falgore
Dan wasan wanda ya taba taka leda a Stoke City da Newcastle United, ya kuma jefa kwallo a wasan karshe na gasar Nations League ta kasarsa a Spain ta lashe.
Real Madrid ta kulla yarjejeniya da shi ne bayan ta raba gari da Karim Benzema wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad da ke kasar Saudiya.
Da ma Real Madid na neman maye gurbin Benzema wanda shi ne dan wasanta na biyu da ya fi ci mata kwallaye a tarihi.
Da fari an yi zaton cewa, dan wasan Tottenham kuma kaften din Ingila, Harry Kane, shi ne zai maye gurbin Benzema
