News
Bashin Da Ake Bin Najeriya Yanzu Ya Doshi Tiriliyan 50 – DMO
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya kai Dala biliyan 103.3, kwatankwacin Naira tiriliyan 49.8 ya zuwa ranar 21 ga watan Maris.
A cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ranar Juma’a, DMO ya ce bashin ya kuma hada da kudaden da ake bin Jihohi da Gwamnatin Tarayya, sai dai ban da wanda Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bin gwamnatin.
DMO ta fadawa Gwamnatin tarayya ta guji abin da zai jawo a nemo bashi a halin da ake ciki Fiye da 70% na abin da ke shigowa cikin aljihun gwamnati ya na komawa ne wajen biyan bashi Hukumar kula da bashin ta bada shawarar a san yadda za a iya domin harajin da ake samu ya karu
Jaridar Vanguard ta ce an fadawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama dole ya gujewa cin bashi.
Hukumar ba ta goyon bayan cin bashi ganin cewa 73.5% na kudin shigan da za a samu a bana duk zai tafi ne a wajen biyan bashin da aka karbo.
DMO ta bayyana, kason kudin shigan da su ke tafiya wajen biyan tsofaffin bashi ya yi yawan da bai dace a sake karbo aron kudi ba.
A fadada hanyar samun kudi Haka zalika hukumar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemi hanyoyin da za tayi wajen ganin ta kara samun kudin shiga a cikin lalitar Najeriya. Idan ana so gwamnatin Najeriya ta iya cin bashi hankali kwance, rahoton ya ce wajibi ne harajin da za a samu a kasafin kudin shekarar nan ya karu.
An yi hasashen samun kudin shiga na Naira Tiriliyan 10.49, DMO ta ce sai gwamnati ta samu abin da ya kai Naira Tiriliyan 15.5 sannan a iya karo bashi.
Wadannan shawara su na cikin gargadin da aka yi wa sabuwar gwamnati bayan nazarin halin kasar. Punce ta ce bashin Najeriya ya doshi N81tr.
Bincike da MAC ta gudanar a kan bashin Najeriya ya nuna kason arzikin kasa ga bashi ya karu zuwa 37.1% a shekarar 2023 bayan ya na 23.4% a 2022. Ko da bashin da ke kan wuyan Najeriya ya karu, binciken ya ce an rage wa’adin lokacin biya.
Abin da masana ke yankewa shi ne ka da bashin da ake biya ya wuce 50% na kudin shigarta, lamarin Najeriya ya yi muni da 73% za su tafi ga biyan bashi. Haka zalika kason jimillar tattalin arziki ga adadin bashi bai dace ya zarce 40%, na Najeriya ya zarce.
Advertisements
