News
Tabbas an bani waje akan titin BUK na siyar, saboda an tabbatar min filin yana kan kaida – Muhuyi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban hukumar yaƙi da rashawa da karɓar koke-koken al’umma ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya tabbatar da cewa gwamnatin da ta gabata ta bashi fili akan titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero dake Kano, kuma ya siyar dashi a lokacin da yake bukatar kuɗi, kuma an tabbatar masa gurin bai saɓa ƙa’ida ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, daya daga cikin mamallakan gine-ginen da ke hanyar BUK, Isma’ila Bello, yayi korafin cewa, shugaban hukumar yaƙi da rashawar ne ya siyar masa da filin, wanda a halin yanzu yana cikin gwamnati mai ci.
Dan kasuwar ya kuma zargi gwamnatin da nuna rashin adalci a shirin rusau da take yi na baya-bayan nan, inda yace wasu daga cikin gine-ginen da aka sanya cikin wadanda za a rusa an same su ne bisa ka’ida daga wuraren mutanen da ke da alaka da gwamnati mai ci.
A ranar juma’a ne dai hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta sanya jan fenti a wasu gine-gine dake kan titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero, wanda ke gaban Ganuwar Kano mai tsohon tarihi a ƙasar Hausa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
