Connect with us

News

Twitter ya ƙayyade adadin saƙonnin da masu amfani da shifan zasu karantawa a rana

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Dandalin sadarwa na Twitter ya ƙayyade adadin saƙonnin da masu amfani da shi za su iya karantawa a rana, a cewar mamallakin kamfanin Elon Musk.

Advertisement

Cikin wani saƙo a Twitter, Mista Musk ya ce shafukan da aka tantantace (masu maki) za su iya karanta saƙo 6,000 a rana ɗaya.

2024:Saudiyya Ta Fitar Da Tsare-Tsaren Aikin Hajjin Badi

A gefe guda kuma, shafukan da ba su da maki za su iya karanta 600 ne kawai.

Advertisement

Cikin wata sanarwa, Musk ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne da zimmar shawo kan “yawan” zirarewar bayanai da kuma daƙile masu bi ta bayan fage.

A ranar Juma’a aka faɗa wa duk waɗanda suka yi yunƙurin karanta saƙo a dandalin cewa dole ne sai sun shiga shafinsu kafin su iya ganin sa.

Advertisement

Matakin “na ɗan loƙaci ne”, in ji Mista Musk

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending