News
NiMet ta yi hasashen samun rana da tsawa daga ranar Litinin zuwa Talata a fadin kasar.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet, ta yi hasashen samun rana da tsawa daga ranar Litinin zuwa Talata a fadin kasar.
Hasashen hukumar ta NiMet, wanda aka saki ranar Lahadi a Abuja, ya nuna cewa daga ranar Litinin rana da tsawa yankin arewacin kasar tare da yiwuwar tsawa da safe a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto.
Jami’ar Jihar Osun ta dakatar da wata daliba da ake zargin tana da hannu a fashin da makami
Haka kuma akwai yiwuwar yin tsawa a sassan jihohin Jigawa, Katsina, Kano, Kaduna, Bauchi, Gombe, Taraba da Adamawa.
“Ana sa ran samun iska mai tsananin yankin Arewa ta tsakiya tare da tsawa a sassan Kwara, Neja, Babban Birnin Tarayya Abuja, Jihohin Nasarawa da Binuwai.
Ana sa ran samun gajimare a kan jihohin Kudu da na gabar teku da ake sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi zuwa sassan jihohin Ogun, Oyo, Edo, Imo, Anambra, Ebonyi, Lagos, Bayelsa, Delta, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
