Connect with us

News

Yan Damfara Na Karbar Kudin ‘Wasu Masu Son Zama Ministoci – Ibrahim Kabir Masari

Published

on

Ibrahim Kabir Masari

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Mai ba wa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu shawarwari kan lamuran siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce wasu ‘yan damfarar siyasa na karbar kudi daga hannun wasu da sunan za su sa shugaba Tinubu ya nada su Ministoci.

Ibrahim Masari wanda Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada shi mai ba da shawara kan siyasa a cikin sabbin mukaman mataimaka 14 da ya fitar, ya ce akwai wadanda ke karbar takardun kwarewar aikin mutane da yaudarar za su kai hukumar DSS da EFCC don tantancewar samun mukamai.

Advertisement

NiMet ta yi hasashen samun rana da tsawa daga ranar Litinin zuwa Talata a fadin kasar.

Ya bayyana cewa suna da rahoto ingantacce cewa akwai wadanda ke ta bi suna karbar kudaden mutane da takardun mutane cewa shugaban kasa ya ce su je su yi tantance mutane ko su zakulo mutanen da za a nada mukamai kmar yanda  muryar amurka ta rawaito cewa wannan magana ba gaskiya ba ne.

Da ya ke magana kan wani jerin sunayen mutane da a ka fito da shi ranar litinin da ke nuna wadanda a ka nada ministoci da hakan bai tabbata ba, Masari ya ce masu gaggawa ne su ka aikata haka da kuma masu marawa wasu baya.

Advertisement

Babban dan siyasar gwamnatin Tinubun ya ce in Tinubu ya dawo zai bayyanawa duniya jerin sunayen ministocin ko kuma za a ji jawabi daga bakin sa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending