Connect with us

News

Fargabar Fuskantar Fari Ta Tilastawa Manoman Jihar Borno Shiryan Addu’ar Rokon Ruwa

Published

on

Fargabar Fuskantar Fari

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Yayinda damunar bana kecigaba da kankama manoma a birnin Maiduguri na jihar Borno na shirye-shiryen gudanar da addu’o’i na musamman kan jinkirin saukar ruwan sama a jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.

Al’amarin ya shafi manoma da galibinsu suka fito daga yankunan arewaci da tsakiyar jihar, inda suka ce suna son a hada kai ne domin neman taimakon Allah kan matsalar.

Advertisement

Yan Damfara Na Karbar Kudin ‘Wasu Masu Son Zama Ministoci – Ibrahim Kabir Masari

Daya daga cikin manoman mai suna Ibrahim Ali ya koka da yadda suke ganin hadari kamar za a yi ruwan sama amma bayan wani lokaci sai ayi iska mai karfi hadarin ya washe.

Arewa radio ta rawaito cewa Majalisar masarautar Borno, tace tana goyon bayan addu’o’in.

Advertisement

A wata sanarwa da ta fitar, Majalisar tace ta hada kan jama’a domin gudanar da addu’o’in rokon ruwan sama na musamman da aka shirya gudanarwa a yau Litinin 17 ga watan Yuli 2023 a dandalin Ramat da ke Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending