Connect with us

News

Gwamnatin tarayya za ta soma aiki da na’ura don karbar haraji daga ‘yan tireda

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Gwamnatin tarayya ta ce za ta soma aiki da kungiyar kananan ‘yan kasuwa domin karbar haraji daga miliyoyin ‘yan tireda a yunkurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kara fadada tattara haraji.

A wata sanarwa da Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya, FIRS, ta fitar a ranar Litinin ta ce tana kokarin hadin gwiwa da kungiyar kananan ‘yan kasuwa ta MATAN domin karbar haraji daga mambobinta.

Kwankwaso: Mutane Sun So Na Rushe Musu Gida Lokacin Ina Gwamna

Ta ce za ta mayar da hankali musamman wajen amfani da na’urori wurin karbar harajin.

Advertisement

Nijeriya na daga cikin kasashen da ake da karancin karbar haraji a duniya inda ake karbar kashi 10.8 cikin 100 kamar yadda FIRS ta bayyana.

Kashi 47 cikin 100 na kasafin kudin 2023 zai fito daga haraji da sauran bangarori na rance.

Kasar, wadda ta fi kowace karfin tattalin arziki a fadin Afirka, ta dauki gagaruman matakai wadanda suka hada da cire tallafin man fetur da cire takunkumi kan hada-hadar kudaden waje, a kokarin gwamnatin ta Tinubu na habaka tattalin arzikin kasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending