Connect with us

News

An Kori Manyan Ƴansanda 3 Da Rage Matsayin Guda 9 Bisa Laifin Rashin Ɗa’a

Published

on

Yan sanda

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar kula da Ayyukan Ƴansanda, PSC, ta amince da korar wasu manyan jami’an ƴansanda uku bisa laifukan rashin da’a da kuma zubar da kimar aikin.

Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

Umarnin Da Kotu Ta Bayar Akan Hana Kama Ganduje, Na Wucin Gadi Ne – Lauya

Ya ce hukumar ta kuma amince da rage matsayin wasu jami’ai su tara da suka hada da kwamishinan ƴansanda.

A cewarsa, hukumar ta dauki wannan matakin ne a yayin taronta na 21, karkashin jagorancin mai shari’a Clara Ogunbiyi, kwamishiniyar shari’a a hukumar.

Mista Ani ya ce Ms Ogunbiyi ce ta jagoranci taron a madadin shugaban PSC, Solomon Arase, wanda daga baya ya shigo taron, wanda aka gudanar ta manhajar Zoom.

Advertisement

Kakakin na PSC ya ce hukumar ta kuma amince da ritayar dole ta wani mataimakin kwamishinan ƴansanda, tare da bayar da umarnin a mayar da duk hakkokin sa da aka biya shi bisa kuskure.

Ya kara da cewa hukumar ta amince da karin girma ga marigayi Insp. Ifeanyi Oroke, zuwa matsayi na gaba na Mataimakin Sufurtandan ƴansanda 2..

Sai dai kuma Mista Ani ya ce hukumar ta kuma maido da wani jami’in da aka kora bisa kuskure, Insp. Augustina Oko, inda ya kara da cewa dawiwar ta ta aiki ta fara tun daga ranar da aka kore ta.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending