News
Umarnin Da Kotu Ta Bayar Akan Hana Kama Ganduje, Na Wucin Gadi Ne – Lauya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Lauya mai zaman kansa a Jihar Kano Barrister Abba Hikima Fagge ya bayyana cewa umarnin da kotu ta bayar na dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na wucin gadi ne.
Barrister Abba Hikima Fagge yace kotu bata da hurumin hana wata hukuma gudanar da aikinta kasancewar doka ce ta samar da ita.
So Shine Farin cikinr Rayuwa haka zalika Shine Matsalar Rayuwa
Sai dai yace kotu tana iya dakatar wa har ta saurari korafin da akayi gabanta kuma daga bisani ta bukaci dukkan bayanai da zasu tabbatar da sahihancin abinda ake dambarwa akansa.
Ya kara da cewa wannan umarni da kotu ta bayar wajibi ne ayi amfani da ita kasancewar zaman doka akeyi, sai dai kuma hakan baya nufun cewa batun binciken ya sha ruwa.
Ya cigaba da cewa abinda kotu ke so shine komai ayi shi akan doka da oda kamar yadda yake cikin tsarin mulki
Yace da zarar hukumar ta karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashwa ta Jihar kano ta gamsar da kotu akan dalilan gayyatar Ganduje to babu shakka babu abinda zai hana Ganduje gurfana a hukumar domin bayar da bayanai.
Wadanda kotun ta umarta da sune hukumar karbar korafe korafe ta jihar kano da kuma Yan sanda sai kuma Civil Depence har sai ta kammala sauraron Karar da tsohon gwamnan ya Kai
A karshe Barrister Abba Hikima yace yanzu babu wanda zai iya yin wani Abu akan wannan batu har sai ta bayyana matsayinta aka korafin da Ganduje ya Kai gabanta.
Idan za a iya tunawa Hukumar Karbar Korafe Korafe da yaki da Cin hanci da rashwa ta Jihar kano tace ta gano sahihancin faifen bidiyon dala da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yana sanyawa a aljihu daga wajen yan kwangila.
Koda yake gwamnan ya sha musantawa yana cewa surkullene na masu hada hotuna.
