Connect with us

News

Ko Shugaban Kasa Tinubu Ya Bani Mukami Bazan Karba Ba – Fayose

Published

on

Advertisements
ads

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya sha alwashin cewa ba zai amince ya karbi mukabin minista daga shugaba Bola Tinubu ba.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels  a daren jiya, Fayose, wanda ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar  PDP a karo na biyu, ya ce bai goyi  bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, a zaben ranar 25 ga Fabrairun 2023.

An Ayyana Dokar Hana Yawo Sakamakon Wata Tarzoma Da Ta Tashi A Jihar Filato

Ya ce ya goyi bayan Tinubu ne saboda ya yarda da shi, ba wai don yana bukatar wani mukami daga gare shi ba.

Ya bukaci Tinubu da ya nada wadanda shekarunsu bai kai 65 ba saboda tsofaffi ne suka kwace makomar matasa kuma lokaci ya yi da ya kamata a baiwa matasa dama.

Advertisement

Ya tabbatar da cewa ya yiwa shugaban kasa Bola Tinubu aiki a lokacin zaben shugaban kasa saboda PDP ta kori dansa.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending