Connect with us

News

Tinubu Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Zaƙulo Masu Kashe Kashe a Filato.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan tashe-tashen hankula na baya-bayan nan da ake samu a jihar Filato.

A cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Dele Alake, shugaban ya yi alla-wadai da rikicin wanda ya janyo kashe-kashen rayuka a ƙaramar hukumar Mangu da kuma wasu kashe-kashen a jihar Benue.

Advertisement

Abin da ya sa har yanzu Tinubu bai nada ministoci ba — Fadar Shugaban kasa

Ya ce “Ana buƙatar haƙuri da yafiya kan kuskuren da wani ya yi matuƙara ana son samar da ingantacciyar al’umma.”

Ya ƙara da cewa “Abin takaici ne yadda jaririya mai watanni takwas a duniya ta rasa ranta sanadiyyar rikicin da ba ta san komai ba a kai a ƙauyen Farin Lamba da ke jihar Filato.”

Advertisement

Ya buƙaci shugabannin al’umma da ƙungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da CAN su haɗa hannu domin samar da mafita ga lamarin.

Shugaban ya kuma umarci jjami’an tsaro da su zaƙulo duk waɗanda ke da hannu a kashe-kashen domin fuskantar hukunci.

Advertisement

Sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta Filato da ta kai ɗaukin gaugawa ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.

A farkon wannan mako ne hukumomi suka ayyana dokar hana zirga-zirga a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato bayan tashe-tashen hankula waɗanda suka yi sanadin rayukan mutane da dama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending