Connect with us

News

Cutar diphtheria ta kashe akalla yara 30 a jihar Yobe

Published

on

Diphtheria

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

Yara akalla yara 30 ne ake fargabar sun mutu, sakamakon kamuwa da cutar mashako ta Diphtheria, yayin da aka kebe 42 a cibiyar killace masu fama da cutar dake asibitin kwararru na karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe.

Advertisement

Tandari, Misau, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Igwanda da Texaco sune wuraren da aka fi zargin wannan cuta ta fi yaduwa.

Tinubu Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Zaƙulo Masu Kashe Kashe a Filato.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, majiya daga cibiyar killace masu fama da cutar, ya shaida cewa suna fama da karancin magunguna.

Advertisement

Ya zuwa yanzu dai a cewar majiyar, mutum 46 aka kwantar, inda mutum biyar daga cikin su suka mutu.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa, yara sama da 20 ne suka mutu a gida, yayin da kuma aka tabbatar da mutuwar hudu a asibiti, sakamakon wannan cuta.

Advertisement

Sai dai, jami’in da ke lura da cibiyar inganta ayyukan rigakafin ta karamar hukumar Potiskun, Mallam Buba, ya shaidawa Daily Trust cewa babu asarar rai da aka samu, amma akwai yara 42 da ke karbar kulawa a asibiti.

Ya kuma bayyana cewa, da dama daga cikin yaran da suka mutu, an gaza mika su asibiti ne akan lokaci.

Advertisement

Babban Daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko na Potiskun din, Mallam Abdurrahman Musa, la’akari da irin bayanan da suke samu game da yaduwar cutar ne, suka gudanar da aikin wayar da kan jama’a domin kaucewa yaduwar annobar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending