Connect with us

News

Majalisar Wakilai Za Ta tantance Manyan hafsoshin da shugaba kasa ya nada

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Majalisar wakilai za ta tantance shugabannin ma’aikatan da aka nada kwanan nan a ranar Litinin.

Advertisement

Channels ta rawaito cewa Manyan hafsoshin da shugaba Bola Tinubu ya nada su ne Maj. Janar Christopher Musa (Babban Hafsan Tsaro), Maj. Janar Taoreed Lagbaja (Babban Hafsan Sojoji), Rear Admiral Emmanuel Ogalla (Babban Hafsan Sojan Ruwa), da AVM Hassan Abubakar (Hafsan Hafsoshin Sojan Sama).

Shara ta tare hanyar sauka daga Gadar sama ta kasuwar Sabon Gari a  Kano.

Zaman dai zai biyo bayan tantancewar da majalisar dattawa ta yi ranar Alhamis tare da tabbatar da nadin shugabannin ma’aikata.

Advertisement

Shugaban majalisar dattijai Godswill Akpabio ya ce, yayin zaman sirrin, hafsoshin sun amsa tambayoyi kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma batutuwan da suka shafi cigaban kasa .

Shugaban kasar a cikin wata wasika da aka karanta a ranar Litinin a zauren majalisar dattijai ya bukaci majalisar ta tabbatar da shugabannin ma’aikatan.

Advertisement

Majalisar dattijai, bayan dawo da zamanta a ranar Alhamis, ta fara tantance hafsan hafsoshin, inda kowannen su ya hau kan dandali domin yin magana kan yadda za su magance matsalar rashin tsaro a kasar nan idan har ta tabbata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending