Connect with us

News

Farashin Litar Man Fetur Ya Karu Zuwa Naira 617 A Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Farashin Man Fetur ya karu zuwa kusan Naira 617 a kowace lita, kamar yadda wakilinmu na birnin tarayya Abuja Philip Nwelih ya tabbatar.

A ziyar da aka kai wani gidan mai na NNPC da ke tsakiyar Abuja, ya tabbatar da cewa yanzu an sauya farashin man daga Naira 539 zuwa Naira 617 kan kowacce lita.

Advertisement

Yawan Amfani Da Man Fetur Ya Ragu A Najeriya

Wani mai abun hawa wanda ya tabbatar wa jaridar karin kudin ya ce ya siya akan Naira 617 kan kowace lita daya.

Har yanzu dai Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya ba ta ce uffan ga manema labarai ba har ya zuwa lokacin da hada wannan rahoto.

Advertisement

Yayinda muke rangadin duba halin da ake ciki a Kano, Arewa Radio ta tabbatar da cewa ana sayar da Litar man akan Naira 620 a wasu gidajen mai.

Wakilinmu Umar Ibrahim Umar wanda yaje daya daga cikin gidajen mai na NNPC Hotoro Kano, domin ganin halin da ake ciki, yace ana sayar da Litar man akan 620.

Advertisement

Sai dai a gidan mai na NNPC dake Club Road a Kano da sauran wasu gidajen mai masu zaman kansu har yanzu ana sayarwa akan Naira 540 zuwa Naira 550.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending