News
Matashi ya shaƙe mahaifiyarsa har ta mutu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Wani matashi ɗan shekara 32, mai suna Samson Sikiru,ya shaƙe mahaifiyarsa har ta mutu a garin Ijebu Ode da ke jihar Ogun.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Omotola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ana dai zargin matashin da tu’ammali da ƙwayoyi.
Karancin Masara Na Neman Durkusar Da Kiwon Kaji A Kasar nan.
Kanin wanda ake zargi da kashe mahaifiyar tasu, wanda yake aikin gadi, shi ya sanarwa makwaɓtansu abin da ke faruwa lokacin da ya dawo ya samu gawar mahaifiyarsu a kwance.
Samson wanda ya kasance ba ya gida na tsawon shekaru, ya dawo ne domin yin bikin babbar Sallah tare da mahaifiyarsa makonni biyu da suka wuce.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an kama matashin ne bayan da makwaɓtansu suka gano cewa shi ya kashe mahaifiyar tasa, inda daga nan aka miƙa shi hannun ƴan sanda.
Kakakin ƴan sandan jihar ta Ogun, Omotola Odutola ta ce matashin yana da lalura ta kwakwalwa.
Ta kuma ce an kasance ana ɗaure lokuta da dama domin kada ya ji wa kansa ko mutane ciwo.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News23 hours ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
