News
Wasu yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe !led Eze Mmirioma, basaraken gargajiya na Aboh Mbaise a jihar Imo a ranar Litinin 17 ga watan Yuli.
Rahotanni na nuni da cewa ‘yan bindigar sun harbe sarkin ne da misalin karfe 3 na yammacin yau. An garzaya da shi asibitin Ndubuisi da ke unguwar inda likitoci suka tabbatar da .
Sarkin Musulmi,Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar Ya Sanar Da Sabuwar Shekarar Musulunci
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya ce.
”Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Imo, CP Mohammed Ahmed Barde psc(+) ya yi Allah wadai da mummunan m¥rder na Eze Mmirioma, wani Basaraken gargajiya a Aboh Mbaise wanda ya mutu a lokacin da ake kula da lafiyarsa a Asibitin Ndubuisi bayan an harbe shi da yawa.
a gidansa a yau da ‘yan bindiga suka yi kuma ya kafa wata babbar tawagar bincike domin gudanar da bincike kan wannan lamari tare da tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da fuskantar fushin doka.”
