News
Hijira: Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Laraba 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Laraba 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye fitar a yau.
Sarkin Musulmi,Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar Ya Sanar Da Sabuwar Shekarar Musulunci
Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar shigowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasar tattalin arzikin jiharmu da kasa baki daya,
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da yin kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabinmu Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.
-
News17 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
