Entertainment
KAMILU K BOY : Abin Da Ya Sa Na Shiga Harkar Waƙa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shahararren matashin mawaƙin nan mai sunan Kamilu Umar , wanda aka fi sani da K Boy Mai Nasara, mazaunin jihar Kebbi wanda ya na ɗaya daga cikin mawaƙan da tauraron su ya fara haske.
K Boy ya kasan ce mutum ne mai ladabi da biyayya ga kowa, ga shi ɗan gaye.
Ya ɗauki tsawon lokaci ya na waƙa, amma sai a cikin shekarar nan ta 2022 aka fara shaida waƙoƙin sa, musamman da komai ya koma ‘online’.
Jaridar INDA RANKA ta tattauna da shi game da rayuwar sa, abin da ya ba shi sha’awa ya fara waƙa, Da kuma alaƙar sa da mawaka kamar Mai gidan sa North Khaleepha da sauran su.
Ya na mai cewa Abin da ya ba ni sha’awa gaskiya yawan sauraren waƙoƙin wasu manyan mawaƙa ne, duba da yadda su ke gudanar da waƙoƙin su cikin hikima da zance, kuma saƙonnin su na zuwa yadda ya kamata to tun daga nan na samu sha’awar abin.
Ya kara da cewa gaskiya ya fuskanci ƙalubale da yawa, daga cikin gidan mu da kuma abokai. Amma kuma ba a iya tunkara na a yi min magana, sai dai a nuna min a fuska da kuma wasu alamomi ba a na’am da abin da na ke yi.
Nayi waƙoƙi da yawa, kama daga siyasa, soyayya, aure, suna, ‘birthday’, da sauran su.
Amma waɗanda na sake su a gari ba za su wuce arba’in ba, musamman na soyayya.
Babban buri na in ga yadda na ke jin wasu manyan mawaƙa, sun samu suna, sun samu kuɗi, waƙoƙi sun shiga ko’ina, sannan kuma a ce ka na da yara a ƙarƙashin ka ka na taimaka masu, burika na kenan.
09052672849
