Entertainment
Hukumar Hisba ta gayyaci Gfresh Al’amin angon Sayyada Sadiya Haruna
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar Hisba ta gayyaci Gfresh Al’amin angon Sayyada Sadiya Haruna Kuma ya amsa Kira yazo Hisba
Hakan ya biyo bayqn Kiran da shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation Amb Auwalu Muhd Danlarabawa yayi akan a gayyato Gfresh Al’amin da Sayyada Sadiya Haruna an samu nasarar amsa wannan Kira Daga Hukumar ta Hisba inda ta gayyato Wanda ake Nema.
Kungiyar Dattawan Arewa Ta Bukaci Tinubu Ya Cire Takunkumin Da Aka Kakabawa Nijar
Gfresh Al’amin ya bayyana a gaban Hukumar Kuma an tattauna dashi akan korafin da muka Kai alhamdulillah saura ita Kuma matar tashi itama zata bayyana a gaban Hukumar Dan itama tayi bayani kamar yadda mijin nata yake
Muna godiya kwarai da gaske ga daukacin al’umma da suka bamu gudunmawa da kiraye kiraye akan wannan lamari, da dukkan kafafen yada labarai da suka bamu gudunmawa Dan samun nasarar wannan lamari na aikin alkhairi ayi umarn da kyakkyawa da hani da mummana.
Muna Kuma Kara Yabawa wannan hukuma data dauki mataki na gaggawa akan wannan Kira da mukayi karkashin kwamanda Mal Ibrahim Daurawa da sauran Ma’aikata na hisaba Daga sassa daban daban da suka bada gudunmawa.
Kuma da yardar Allah zaaji yadda ta kasance Anan gaba Daga ita kanta wannan hukuma.