Connect with us

Entertainment

NDLEA ta nada Naira Merly shugaban yaƙi da shan miyagun kwayoyi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA ta nada shahararren Mawakin kasar nan Azeez Adeshina Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley a matsayin shugaban yaƙi da shan miyagun kwayoyi.

Naira Marley bayan ya sanar da haɗin guiwarsa da Hukumar ya roƙi masoyansa da aka fi sani da Marlians da su daina shaye-shayen kwayoyi.

Advertisement

Babangida Ya Bar Abin Alfaharin Da Ba Za A Taba Mantawa Da Shi Ba A Najeriya–Tinubu

Mawakin ya yi wannan roko ne a ranar Alhamis bayan ya kammala kulla sabon kawance da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA a gangamin da suke yi na yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin.

A cewar mawakin, shan miyagun kwayoyi kan haifar da cututtuka sannan kuma sukan iya kai mutum ga aikata laifuka.

Advertisement

Haka kuma ya bayyana cewa ya shiga gangamin yaƙi da shan miyagun kwayoyi ne saboda aniyarsa na ganin an tsaftace ƙasar daga sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi.

Ya ƙara da cewa zai so yayi yi kira ga magoya bayansa, Marliyans da dukkan matasan Najeriya da su daina shan miyagun ƙwayoyi domin ba shi da kyau kuma yana karya garkuwar jiki, yana mai ƙara yin kira a gare su da su shigo cikin tafiyar domin kawar da ta’ammuli da miyagun kwayoyi a tsakanin matasan mu.

Advertisement

Sai dai kuma wata Fitacciyar Jarumar fina-finan Nollywood, Tonto Dikeh, ta mayar da martani kan matakin da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA ta ɗauka na shigar da mawaƙinl Naira Marley a yakin da take yi da shan miyagun kwayoyi.

Jarumar ta bayyana a shafinta na instagram cewa matakin abin kunya ne.

Advertisement

Tace wannan shine babban abin kunya da ta ga wata hukuma ko Ma’aikata tayi da ke rajin hana shan miyagun kwayoyin tana mai la’akari da Naira Marley a matsayin babban Ɗan shaye-shaye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending