News
Gwamnan jahar Kano Ya Kara Nada Mutane 42 A Matsayin Masu Temaka Masa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada karin wasu mutane 42 a matsayin masu temaka masa da kuma bashi shawara.
Sanarwar da kakakinsa Sanusi Bature ya fitar a daren jiya, Ya ce wadanda aka nada kan mukaman, sun hada da, Yusuf Ibrahim Sharada a matsayin babban mataimakin gwamna kan bangaren fasahar sadarwar zamani.
Hukumar ICPC Ta Fara Bincike Kan Zargin cin Hanci da Rashawa Da ake Yiwa Tsohon Ministan Shari’a
Kazalika gwamnan ya nada Muhammad Sani Hotoro a matsayin babban mataimakinsa ta bangaren kungiyoyin hadin kai, Sai Barrister Nura Abdullahi Bagwai a matsayin babban mataimakinsa a bangaren shari’a, Sai Hon Surajo Kanawa a matsayin babban mataimakin gwamna ta bangaren wayar da kan jama’a a bangaren Kano ta Kudu.
Shi kuwa Muhammad Sani Salisu Riming ado shine babban babban hadimin gwamna a bangaren wayar da kan jama’a a shiyyar kano ta Arewa, yayin da Nuhu Isa Gawuna zai rike irin wannan matsayi a kano ta tsakiya da sauran mutane daban daban da gwamnan ya nada kan mukamai na siyasa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
