Connect with us

News

Sojojin Jumhuriyar Nijar sun naɗa sabon Firaminista

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Jagoran sojojin jumhuriyar  da suka yi juyin mulki a Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya sanar da tsohon ministan kuɗin ƙasar a matsayin sabon firaminista.

Ali Mahaman Lamine Zeine ya maye gurbin Mahamadou Ouhoumoudou wanda yake Turai lokacin da aka yi juyin mulkin.

kungiyar kwadago ta NLC Ta Janye Shirinta Na Fara Yajin Aiki

Mista Zeine, ya rike muƙamin ministan kuɗi daga shekara ta 2001 zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatin tsohon shugaba Mamadou Tandja a 2010.

Ya taɓa yin aiki a bankin bunƙasa Afrika, a ƙasashen Chadi da Ivory Coast da kuma Gabon, kuma shi ne ya mallakin kamfanin yaɗa labarai na ActuNiger.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending