News
Tsohon Dan Jarida Mato Adamu ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shahararren dan jarida kuma tsohon ma’aikacin Sashen Hausa na BBC, Mato Adamu, ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
Majiyar ‘yan uwa ta bayyana cewa, fitaccen dan jaridan ya rasu ne da yammacin Juma’a a Asibitin kwararru dake Gombe bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Bayan ya bar BBC, ya yi aiki a matsayin ɗan jarida mai zaman kansa tare da ƙungiyoyin watsa labaru na duniya da dama, ciki har da Reuters.
Ya kasance dan asalin karamar hukumar Dambam ta jihar Bauchi, amma marigayi Mato Adamu da ke jihar Gombe, ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkokin yada labarai.
Ya yi aiki a takaice a matsayin babban mai ba Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe shawara kan harkokin yada labarai, a lokacin mulkin gwamnan na farko.
An shirya sallar jana’izarsa a yau Asabar da karfe 11 na safe a asibitin kwararru dake Gombe
-
News19 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
