News
Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta ceto kayayyaki da kadarori na miliyoyi a wata gobara da ta tashi a garin Ilorin
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta ceto kayayyaki da kadarori na Naira miliyan 6.6 a wata gobara da ta tashi a garin Ilorin na jihar Kwara a ranar Asabar.
Jaridar Daily post ta rawaito cewa Lamarin ya faru ne da misalin karfe 01:05 a Unguwar Ile-Kowope Olorunkuse da ke Offa a karamar hukumar Offa.
Wani mai kiran da ba a bayyana sunansa ba ne ya sanar da hukumar kashe gobara, wanda ya yi ikirarin cewa yana zaune kusa da wurin da gobarar ta tashi.
Jami’an kwana-kwana sun samu nasarar kashe gobarar a kan lokaci sannan kuma daga cikin falo mai dauke da daki biyu da shaguna hudu da ke cikin ginin.
A cewar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Hassan Adekunle, gobarar ta tashi ne a sanadiyar wata wutar lantarki.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bukaci kada su yi kasa a gwiwa wajen kiran hukumar kashe gobara a cikin gaggawa.
