News
Hukumar NDLEA ta Kame Wasu Mutum 10 da Ake Zargin Dillalan Miyagun Kwayoyi Ne A Kano

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshi jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 10 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne da ke gudanar da ayyukansu a sassan jihar a watan Yuli kadai.
Sadiq Maigatari, jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA na jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.
Maitagari ya ce wadanda ake zargin sun hada da Abubakar Yunusa mai shekaru 33, James Temitope mai shekaru 42, Sani Muhammad dan shekara 23, Aminu Sani 23 da Emeka Williams mai shekaru 31.
DA DUMI-DUMINSA: Farashin Masara Ya Sauka A Adamawa Daga Dubu 67 Zuwa Dubu 48
Ya ce sauran wadanda ake zargin sun hada da Inusa Alhassan mai shekaru 31 da Muhammad Abubakar 35 da Hussaini Hamza 45 da Sani Dahiru 30 da kuma Muhammad Ibrahim mai shekaru 30.
Maitagari ya ce an kama wasu daga cikin mutanen da ganyen da ake zargin tabar wiwi ce yayin da wasu kuma an kama su da allurar pentazocine guda 2,000 da kuma kwalabe 48 na codeine mai nauyin kilogiram 4.8.
Ya ce ayyukan da suka kai ga kame miyagun kwayoyi tare da kame dilolin da ake zargin sun dakile rarraba kayan a jihar tare da kawar da adadi mai yawa daga yaduwa.
“Ilolin da wannan adadin haramtattun abubuwa zai iya haifarwa ba shi da ƙima.
“Wannan ba shakka zai kawo cikas ga kasuwannin haramtattun muggan kwayoyi, da kuma kare al’umma daga illar da haramtattun abubuwa ke haifarwa,” in ji shi.
Maitagari ya yi kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga hukumar NDLEA domin tabbatar da jihar Kano ba ta da kwaya ga zuriya masu zuwa.