News
Manyan ƙalubalan da ke gaban sabbin ministocin tsaron Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tun a ranar Litinin, jim kaɗan bayan rantsar da su, ministocin Shugaba Bola Tinubu, suka fara aiki gadan-gadan.
Shugaban na Najeriya ya ce ya zaɓo ministocin ne, bisa cancanta.
Kano Poly ta ƙaddamar da Gudanar da shirye-shiryen BSc, PGD da kuma MSc,
Ɓangarorin da ga alama, aka fi sanya wa ido don ganin yadda sabbin ministocin za su tunkari matsalolin ma’aikatunsu da kuma shawo kansu, akwai tsaro.
Duk sabbin ministocin tsaron guda biyu, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, ba su da gogewar aiki a ɓangaren.
Masharhanta sun ce naɗa su, matsayin manyan masu jagorantar harkar tsaro a Najeriya, na cikin naɗe-naɗen Tinubu mafi bazata da ban mamaki ya zuwa yanzu.
A tsawon rayuwarsa, babban ministan tsaron, ya buɗi ido ne a fagen kasuwanci da masana’antu, kafin ya faɗa siyasa. Shi ma, Matawalle dai sammakal, tsohon malamin makaranta ne.
Babban ministan tsaron dai, ya shaida wa BBC jim kaɗan bayan rantsar da shi a Abuja, cewa ya yi gwamna tsawon shekara takwas, kuma duk wanda ya kasance babban jami’in tsaro na jiha tsawon shekaru, ba shakka yana da gudunmawar da zai bayar a ɓangaren tsaro.
A cewarsa, ba karatu ba ne kawai aikin tsaro, a matsayinsa na mashahurin ɗan kasuwa, ya naƙalci tattaro rukunin ƙwararru.
Babban sirrin aiki irin wannan, shi ne: “Iya haɗa rukunin ƙwararrun da za su ba da shawara a kan abin da ya dace.” Kuma da yardar Ubangiji, za mu haɗa waɗannan mutanen, waɗanda za su ba mu shawara a samu sauƙin matsalar tsaro”.
Ɗumbin ‘yan Najeriya ne za su raka wannan fata na sabon ministan tsaron ƙasar da addu’ar ‘amin’.
To amma, ko waɗanne ƙalubalan tsaro ne suka fi ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya?
1- Juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar
2- ‘Yan fashin daji
3- Boko Haram
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
