News
Indaranka:Yadda Ɗan shekara 94 ya yi wa Ƴar shekara 13 fyade
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA.
An kama wani dattijo mai shekaru 94 a jihar Adamawa bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta samu da yammacin jiya Laraba, inda ta ce jami’anta sun kama mutumin mai suna Mohammed Abubakar da aikata wannan aika-aika a unguwar Tappare da ke garin Ganye, hedikwatar karamar hukumar Ganye a Kudancin Adamawa.
SAMAR DA TSARO: Gwamnatin Kaduna za ta dauki matasa ‘yan sa kai 7,000
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar dauke da sa hannun PRO, SP Suleiman Nguroje, ta ce wanda ake zargin mai sana’ar sayar da ganye, ya yi kaurin suna wajen yaudarar yara mata ta hanyar ba su sukari da sauran kayan zaki.
“Ya faru ne a ranar 12 ga Agusta, 2023, yayin da wanda aka yi wa fyaɗe ke wucewa ta gidan wanda ake zargin, ya kira ta zuwa cikin gidan kuma ya ci zarafinta ta hanyar sanin ta na zahiri da ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wanda ake zargin yayin da yake aikata wannan aika-aika, ya shafa mata wani kamshi da turare, wanda hakan ya sa wanda aka azabtar ta samu rashin lafiya bayan afkuwar lamarin.”
Ya ce yarinyar ta bayyana hakan ne a lokacin da mahaifiyarta ta yi mata tambayoyi game da rashin lafiyarta, inda daga nan ne aka kai rahoton lamarin zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Ganye.
“Kwamishanan ‘yan sanda, Afolabi Babatola, wanda ya fusata kan wannan mumunan lamarin, ya umurci jami’in da ke kula da sashin tallafawa iyali na rundunar da ya dauki nauyin gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da wanda ya aikata laifin,” in ji ‘yan sandan.