Connect with us

Business

Kamfanonin Kasar Nan Sun Samu Naira Bilyan 55 Saboda Hana Shigo Da Layin Waya

Published

on

Layin waya
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Hukumar Sadarwa ta kasa, NCC, ta bayyana cewa masana’antun cikin gida sun samu kudaden shiga da ya haura Naira bilyan 55 sakamakon hana shigo da Layukan waya cikin kasar nan.

Idan za a iya tunawa, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a yayin wani bikin baje kolin kayayyakin sadarwa da aka gudanar a shekarar da ta gabata, ya sanar da hana shigo da layukan waya cikin kasar nan.

Advertisement

Ana fargabar mutuwar mutane da dama, wasu kuma sun makale a yayin da wani bene mai hawa biyu ya rufta a Abuja

Da yake tsokaci kan irin nasarorin da hukumar ta samu wajen inganta abubuwan da suka shafi cikin gida, Shugaban hukumar sadarwa ta kasa Farfesa Umar Garba Danbatta, ya ce hana shigo da layukan waya daga kasashen waje, ya temaka wajen saukaka bukatar samun kudin kasashen waje a kasar nan.

Ya kara da cewa haramcin ya temakawa yan kasuwar gida masu kera Layin waya da kansu wajen samun kudin shiga har Naira biliyan 55 .

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *