Politics
Yadda ‘yan jam’iyyar APC suka yi zanga-zanga a Abuja
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Bayanai na kara fitowa kan dambarwar da ta tashi a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja a ranar Alhamis, inda ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka yi cincirindo don hana wasu ‘ya’yan jam’iyyar gudanar da zanga-zanga a harabar.
Bbc ta rawaito cewa Wasu ‘ya’yan jam’iyyar daga jihohin Edo da Bayelsa ne suka yi turuwa zuwa hedikwatar jam’iyyar.
Rugujewar Gini: Tinubu da Wike Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja
Masu zanga-zangar dai, na nuna rashin amincewa da sabbin zaɓin da jam’iyyar ta yi na shugabannin da za su maye gurbin wadanda suka sauka.
A ranar 3 ga watan Agusta ne kwamitin gudanarwar jam’iyyar APCn na kasa ya sanar da sabbin naɗe-naden, bayan kammala wani taro a Abuja.
A lokacin, jam’iyyar ta sanar da naɗin Ali Dalori a matsayin wanda zai maye gurbin sanata Abubakar Kyari da ya sauka daga mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa.
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya kuma amince da naɗin Dakta Mary Idele a matsayin shugabar mata ta jam’iyyar don maye gurbin Dakta Betta Edu wadda ta zamo minister jin-kai da kawar da talauci ta Najeriya.
Wadanda suka shaida abin da ya faru a hedikwatar jam’iyyar a ranar Alhamis dai sun ce cikin fushi gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya shiga ofishin kuma ko da ya fita babu wata alama da ke nuna ya yi sanyi.
Gwamnan jihar Kogin dai yana turjiya ne ga zaɓin da uwar jam’iyya mai mulkin ta yi, na naɗin Hon Duro Mesoko daga jihar Kogin a matsayin mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa, a madadin Yahaya Ismail da ya nemi a naɗa.
Irin wannan dambarwa a wajen naɗin shugabannin jam’iyya ba sabon al’amari ba ne a Najeriya, amma wannan zai iya zama gwajin farko ga sabon shugaban jam’iyyar APCn na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, kuma duniya ta zura ido don ganin yadda zai shawo kan wannan matsala.
