News
Ƴan sandan Kano sun sanya Naira miliyan 1 ga duk wanda ya kawo labarin yan daba biyu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ƙara kudi kan kawo bayanan wasu fitattun ‘yan daba da ke cikin jerin sunayen da ta ke nema ruwa a jallo daga Naira 100,000 zuwa N500,000 kowanne.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika wasu tubabbun ‘yan baranda 100 ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a filin wasa na Sani Abacha a yayin bikin rufe gasar kwallon kafa ta ‘yan sanda ta farko da rundunar ta shirya tare da Ƙungiyar Matasa don Rigakafin Cututtuka da Mutuwar Jama’a (YOSPIS).
Ƴan sandan Kano sun sanya Naira miliyan 1 ga duk wanda ya kawo labarin yan daba biyu
Sai dai CP Gumel, ya sha alwashin cewa rundunar ‘yan sandan za ta yi duk mai yiwuwa domin gurfanar da su a gaban kuliya, yayin da ya tuna cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta kaddamar da farautar wasu mashahuran mutane uku, inda daya daga cikinsu ya mika kansa.
Kwamishinan ‘yan sandan wanda ya gabatar da tubabbun ‘yan daba 100 ga Gwamna Yusuf domin gyarawa da kuma kara musu karfin gwiwa, sai dai ya bukaci al’umma da kada su rika kyama ga tubabbun daban kamar yadda suka yi alkawari za su juya baya ba za su sake komawa ga aikata laifuka ba.
A cewarsa, “Lokacin da na hau aiki, an samu yawaitar laifukan fashi da makami, sace-sacen waya da sauran munanan laifuka a jihar.
“Manufar gasar kwallon kafa ita ce a samar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin jami’an tsaro da matasa a jihar, musamman ‘yan daba da suka tuba a wani yunkuri na ganin an ji ana son su da kuma dawo da su cikin al’umma.