Connect with us

News

Babu adalci a rabon tallafin miliyan 500 da matar shugaban ƙasa ta bayar a Plateau

Published

on

Remi Tinubu
Spread the love

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI l, reshen Jihar Plateau, ta yi zargin cewa an ware ta daga wadanda su ka ci gajiyar tallafin Naira miliyan 500 da uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta bayar.

Advertisement

A jiya Talata ne Remi Tinubu ta kai ziyarar jaje jihar, inda ta bayyana bayar da tallafin Naira miliyan 500 ga iyalai 500 da rikicin Plateau ya shafa a kananan hukumomin Mangu da Bokkos da Barikin Ladi da Riyom da kuma Jos ta Kudu a jihar.

Kotu Ta Tsare Wani Matashi A Kan Zargin Satar Tunkiya A Jahar Kano

Sai dai JNI a cikin wata sanarwa da Daraktanta na harkokin fasahar zamani da kungiyoyi masu zaman kansu, Lawal Ishaq ya fitar, ta yi zargin cewa an yi rashin adalci a jerin sunayen iyalan wadanda suka ci gajiyar tallafin.

Advertisement

A cewar sanarwar, babu musulmi guda ɗaya da ya amfana da tallafin a cikin jerin.

Hakan ya sanya shakku kan gaskiyar gwamnatin jihar Plateau na samar da dawwamammen sulhu a rikicin jihar, JNI ta yi zargin nuna ɓangaranci wajen hada jerin sunayen wadanda suka ci gajiyar tallafin.

“Da yawa daga cikin shugabannin addinin Musulunci da kuma Fulani makiyaya sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda aka cire musulmi gaba daya, da kuma karkatar da jerin iyalai 500 da rikicin da ya rutsa da su a kananan hukumomi biyar na jihar Plateau.

Advertisement

“Abin takaici, da yawa daga cikin shugabannin Musulmi da Fulani, lokacin da gwamnatin jihar Plateau ta fitar da jerin sunayen wadanda suka ci gajiyar tallafin, babu wani musulmi guda daya da aka saka.

JNI ta kara da cewa “Wannan abin bakin ciki ne, domin a rubuce yake cewa, akwai Musulmai da dama da suka hada da Fulani makiyaya da rikicin ya raba da muhallansu, musamman a karamar hukumar Mangu inda rikicin ya koma na addini,” in ji JNI.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *