Connect with us

News

Ana fargaba fiye da mutum 20,000 sun mutu a bala’in ambaliyar Libya

Published

on

Inda ambaliyar ruwa ya rusa
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAH

Sama da mutum 20,000 ne ake fargabar cewa sun mutu a ambaliyar ruwan Libya, a cewar wani jami’in gwamnatin yanki.

Bala’in ambaliyar ruwan ya shafe gabashin ƙasar ranar Lahadi.

Advertisement

Magajin birnin Derna na gaɓar teku ya faɗa wa tashar talbijin ta Saudiyya mai suna Al Arabiya cewa ya yi ƙiyasi kimanin mutum 18,000 zuwa 20,000 ne suka mutu lokacin da madatsun ruwan birnin suka fashe, inda ambaliyar ruwan tsunami ta yi awon gaba da mutane a lokacin da suke gida suna barci.

Babu adalci a rabon tallafin miliyan 500 da matar shugaban ƙasa ta bayar a Plateau

Alƙaluman da ya bayar sun dogara ne a kan adadin unwagunnin da ambaliyar ta ɗaiɗaita, kamar yadda ya faɗa wa gidan talbijin ɗin.

Advertisement

Gawawwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu na ƙarƙashin ɓaraguzai ko kuma can a cikin teku, lamarin da ke ƙara kasadar ɓarkewar cutuka.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce gwamnatoci biyu da ke gaba da juna a Libya suna aiki tare, wajen tsara aikin taimakon mutanen da mummunar ambaliyar ruwa ta faɗa wa a kwana huɗu da ya gabata.

 

Advertisement

Hukumomin biyu, da wadda ke mulkin yammacin ƙasar da kuma mai mulki a gabashi inda bala’in ya auku sakamakon mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da aka yi wa laƙabin Daniel, suna ta kira ga hukumomi da ƙasashen duniya su agaza.

Ana ta samun ƙaruwar waɗanda suka mutu, bayan sama da dubu biyar da aka tabbatar zuwa yanzu.

Jami’ai na ganin yawan waɗanda bala’in ya hallaka zai iya kaiwa kusan dubu uku.

Advertisement

A ranar Lahadi wannan bala’i na ambaliya da ke kama da Tsunami, ya afka wa ƙasar ta Libya a ɓangaren gabashi.

Ambaliyar ta haddasa ɓallewar madatsun ruwa da gadoji a birnin Derna inda lamarin ya fi ta’adi.

Hukumomin ƙasar biyu da ba sa ga maciji da juna, a yanzu sun kawar da wannan gaba, inda suka zamanto kamar ciki ɗaya wajen tsara aikin agaji.

Advertisement

Gwamnatin da ke iko da yammacin Libya wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ita, na dafa wa abokiyar gabar tata da ke gabashi, inda bala’in ya afku.

Hukumomin biyu na ta kira ga ƙasashen duniya da su taimaka, yayin da teku ke ta angizo tarin gawarwakin mutanen da ambaliyar ta hallaka.

Masu aikin agaji na ta faman suturta su, bayan iyalai da ‘yan uwa sun gane nasu, ana kuma binne su a manyan ƙaburbura na bai-ɗaya.

Advertisement

Kusan a ko da yaushe ƙaruwar alƙaluman waɗanda suka rasu ake yi, da bayyana ko gano wasu ƙarin gawarwaki, bayan sama da dubu biyar da ɗari uku da aka samu a birnin Derna.

Tauhid Pasha na hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi wa BBC bayani kan yadda gwamnatocin biyu na ƙasar ke aiki tare:

Ya ce, abin mamaki ne a ce, gwamnatocin biyu na kira ga hukumomin duniya suna neman taimako.

Advertisement

Ƙalubalen yanzu shi ne ƙasashen duniya su amsa yadda ya kamata ga buƙatu da kiran na gwamnatocin.’’

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *