Connect with us

News

An Kaddamar Da Kwamitin Bikin Cikar Kasar nan Shekara 63 Da Samun ‘Yancin Kai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutane 15 domin shirya bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, wanda ya kaddamar da kwamitin a ranar Alhamis a Abuja, ya kuma kaddamar da ayyukan da aka tsara za’a gudanar domin bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Gayyaci Shugabannin APC Da NNPP, Gabanin Hukuncin Kotu Kan Zaben Gwamna A Kano

Akume wanda shi ne shugaban kwamitin ya ce za a gudanar da Abubuwan da aka tsara don gudanar da bikin ne da kwamitin zai kammala.

Ya ce an kafa shi ne don tsarawa da aiwatar da duk wasu ayyukan da aka amince da su da suka dace da bikin cikar Nijeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, na 2023.

Wqni labarin kuma 2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Gayyaci Shugabannin APC Da NNPP, Gabanin Hukuncin Kotu Kan Zaben Gwamna A Kano

Advertisement

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending