News
Har Yanzu Babu Takamaimiyar Ranar Dawo Da Ayyukan Jiragen Daular Larabawa A Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin tarayya ta janye sanarwar da ta yi tunda farko dangane da dawo da zirga-zirgar jiragen sama daga Hadaddiyar Daular Larabawa da Etihad Airlines a Najeriya.
Ministan sufurin jiragen sama da kula da sararin samaniya, Festus Keyamo, ya ce babu wani lokaci da aka tsayar da kamfanonin jiragen biyu za su ci gaba da zirga-zirga a Najeriya.
An Kaddamar Da Kwamitin Bikin Cikar Kasar nan Shekara 63 Da Samun ‘Yancin Kai
Wannan sanarwar ta ci karo da sanarwar farko da mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale ya bayar bayan ganawar da shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa na daukar larabawa Sheik Mohamed bin Zayed Al Nahyan, a ranar Litinin.
Ngelale ya ce bayan ganawar kamfanin Emirates Airline zai ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai Keyamo wanda ya yi magana a taron kolin jiragen sama na Afrika da aka rufe a Abuja ranar Alhamis, ya ce ana kan kammala yarjejeniyar
Wani labarin kuma An Kaddamar Da Kwamitin Bikin Cikar Kasar nan Shekara 63 Da Samun ‘Yancin Kai
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
