News
Tinubu ya nada Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan CBN

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Kasar, CBN.
Ya bayyana haka ne a sanarwar da mai magana da yawunsa Chief Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a.
Jami’ar Chicago ta fitar da sanarwa kan bayanan karatun Tinubu
Olayemi Michael Cardoso ya maye gurbin Godwin Emefiele wanda Shugaba Tinubu ya dakatar daga mukaminsa kuma ake tuhumarsa da badakalar biliyoyin kudade.
Kazalika Shugaba Tinubu ya amince da nadin sabbin mataimakan gwamnan CBN guda hudu. Mutanen su ne Mrs. Emem Nnana Usoro, Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Mr. Philip Ikeazor da Dr. Bala M. Bello.
Gwamnan na CBN da mataimakansa za su yi wa’adi ne na shekara biyar, a cewar sanarwar.
A watan Yuni ne Shugaba Tinubu ya dakatar dakatar da Mr Emefiele daga shugabancin CBN, sannan ya bayar da umarni a gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.
Daga nan aka mika ragamar tafiyar da bankin a hannun mataimakinsa Mr. Folashodun Adebisi Shonubi.
Godwin Emefiele ya aiwatar da sauye-sauyen da suka jawo ce-ce-ku-ce a fannin tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2022, ya sauya fasalin takardun naira 200, 500 da kuma 1,000 da zummar rage hauhawar farashin kayayyaki da yin kudin-jabu da kuma biyan kudi ga masu garkuwa da mutane.
Sai dai matakin ya jefa ‘yan kasar cikin mawuyancin hali sannan ‘yan siyasa sun bayyana cewa an fito da shi ne da
Wani labarin kuma Jami’ar Chicago ta fitar da sanarwa kan bayanan karatun Tinubu
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
zummar cin zarafinsu.