News
Yan Kwankwasiyya Sun Gudanar Da Sallar Samun Nasara A Kotun Zabe.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Daruruwan ‘yan kungiyar Kwankwasiyya ne suka hallara a Kano a ranar Alhamis domin gudanar da addu’o’i na musamman domin samun nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a kotun sauraron kararrakin zaben Gwamna.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Jam’iyyar adawa ta APC na kalubalantar nasarar da Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu a zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Yan Majalissar Wakilai Sun Musanta Karbar Tallafin Rage Radadi Na Milliyan 100 Kowannensu
Sai dai a yayin da kotun ke shirin yanke hukunci kan rikicin zaben gwamna, ‘yan Kwankwasiyya na neman sa hannun Allah.
Sallar wacce ta kunshi maza da mata mabiyan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, an gudanar da addu’o’in ne a titin Zaria, Maiduguri, Hadejia da Gwarzo wadanda su ne manyan hanyoyin shiga birnin na dabo ba gari ba dajin Allah
Da take jawabi a daya daga cikin wuraren addu’o’in, shugabar kungiyar mata ta NNPP ta jihar, Hajiya Zuwaira Abubakar, ta yi ishara da cewa suna addu’a ga wadanda suke da niyyar tsige Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.
Ta ce muna sane da irin yadda aka yi kaurin suna da aikata laifuka a karkashin kasa domin kwace nasarar da gwamnatin NNPP ta yi mana a jihar Kano da kuma rokon Allah da ya dauki nauyin masu wannan yunkuri.
Abubakar ta bayyana cewa ba za su bari wasu da ba su ji dadi su dauke nasarar Yusuf a zaben gwamna.
Ta bayyana nasarar da gwamnan ya samu a zaben a matsayin farin jini domin kuwa dukkan kanawa sun fito ranar zabe sun nuna cewar suna tare da Abba Kabir Yusuf kuma suna tare da jagoran kwankwasiyya Rabiu Musa inji Zuwaira.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
