News
Yan Majalissar Wakilai Sun Musanta Karbar Tallafin Rage Radadi Na Milliyan 100 Kowannensu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Majalisar wakilai ta yi watsi da wata sanarwa daga mataimakin sakataren kungiyar kwadago ta kasa NLC, Christopher Onyeka cewa kowanne mamba ya samu Naira milliyan 100 amatsayin tallafi.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Akin Rotimi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Wata Ta Kardama Ta Kunno Ka Tsakanin Gwamnati Da Makarantu Masu Zaman Kansu A Jihar Kano
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Idan za’a iya tunawa Onyeka ya yi ikirarin a ranar Talata cewa bangaren zartaswa ya baiwa kowane dan majalisar tarayya Naira miliyan 100 amatsayin tallafi.
Da yake mayar da martani, Rotimi ya ce wannan ikirari ba shi da tushe balle makama.
Ya nuna shakku kan ko Onyeka na wakilcin kungiyar NLC a hukumance kan ikirarin, ya kara da cewa duk da haka yana da muhimmanci a gyara irin wadannan bayanai.
Wani labarin kuma Wata Ta Kardama Ta Kunno Ka Tsakanin Gwamnati Da Makarantu Masu Zaman Kansu A Jihar Kano
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
