News
An Kama Wata Mata Da Muggan Kwayoyi A Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA), Kano, sun cafke wata mata mai suna Bilkisu Mohammed Bello, ‘yar shekaru 45 da haihuwa, dauke da faleti 52 na hodar iblis a yayin da take shirin shiga jirgin saman Saudia zuwa kasa mai tsarki.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar Femi Babafemi ya fitar ta ce an kama wadda ake zargin ne a ranar Talata.
Sanarwar ta ce, ”Lokacin da aka zanta da ita, ta amsa cewa kwalayen hodar iblis da aka ba ta boye kafin lokacin tashin jirginta a wani gida da ke unguwar Farawa a Kano.
‘’Lokacin da ta jagoranci jami’an NDLEA zuwa gidan, an samu kundi 52 na haramtattun kayan da nauyinsu ya kai gram 767.
“A halin da ake ciki kuma, an kama wani da ake zargi mai suna Auwal Bindow a ranar Juma’a a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe dauke da kwayoyin maye na tramadol 50,000, yayin da a Jihar Oyo kuma jami’an NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, suka kama Anuoluwapo Blessing Iyanu mai shekaru 32, tare da katan 52 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 30 a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba.
“Hakazalika, jami’an NDLEA hadin gwiwa da jami’an Sojojin Najeriya, hukumar Tsaron Najeriya da hukumar kula da kadarorin gwamnati NSCDC da kuma jami’an Amotekun a ranar 3 ga watan Oktoba, sun kai farmaki garin James, da ke Ogunmakin, a karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun inda suka gano tare da lalata tan 10.38. na tabar wiwi da ke rufe sama da kadada 4.152.
“A yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga aikin, rundunar ta kuma kama wata mota mai lamba FS548XN dauke da kwantena 40ft mai dauke da guma-guman katako.
“Binciken da aka yi wa kwantena ya kai ga gano buhunan tabar wiwi mai nauyin kilogiram 20, yayin da aka kama mutane shida: Ahmed Yusuf, Olaniyi Babatunde, Adedeji Babatunde, Richard John, Osolale Olamilekan da Abdulazeez Saied, a cikin motar.
