Connect with us

News

Gwamnatin jihar Kano za ta samar da kyakkyawan yanayi ga sabon shirin SFH

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Advertisement

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin samar da yanayin da za a samu nasarar aiwatar da shirin dakile cutar kanjamau na KP-CARE-2 (Key Population Community HIV Service for Action and Response), wani sabon shiri na na Kungiyar kula da Lafiyar Iyali (Society for Family Health, SFH) don taimakawa wajen dakile yaduwar cutar HIV a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar tawagar SFH a ofishinsa domin yi masa bayanin shirin.

Advertisement

Abubuwa 5 Game Da Sabon Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ibrahim Abdullahi, jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.

Kwamishinan ya kara da cewa, akwai dadaddiyar alakar aiki tsakanin jihar Kano da SFH, ya kuma yaba da irin kyawawan ayyukan da suka yi wa jihar da ma kasa baki daya, ya kara da cewa sabon shirin zai kasance a Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta jihar Kano, saboda Hukumar tana da ƙwararrun mutane da ke dukkan ƙwarewar da SFH ke bukata.

Advertisement

Ya kuma bai wa hukumar SFH tabbacin gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali a jihar Kano, inda ya yaba musu bisa yadda suke aiki a cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko ta hanyar samar da kayan aiki da horar da ma’aikata wanda ya bayyana hakan a matsayin hanya mai kyau ta samar da ayyuka masu inganci.

Kwamishinan ya kuma yaba da yadda suka hada da samar da maganin cutar kanjamau kyauta a cikin shirin, inda ya ce hakan zai taimaka matuka wajen rage wahalar da ake fuskanta na rashin wasu magunguna, domin a halin yanzu akwai magungunan da ke da wuyar samu a fadin kasar nan duk da amincewa da sakin kudaden da gwamnatin jihar ta yi.

Advertisement

Dakta Labaran ya bayyana jin dadinsa kan matakan da mai girma gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dauka na farfado da fannin kiwon lafiya na jihar

Tun da farko, babban jami’in SFH na shirin KP-CARE-2, Mista Abdussamad Salihu, ya bayyana cewa shirin ya shafe shekaru hudu a Najeriya a jihohi shida da suka hada da Adamawa, Bauchi, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Borno.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa, bisa la’akari da irin nasarorin da aka samu a wadannan jihohi, an kara fadada shirin zuwa jihohin Kano da Taraba a shekarar da ta gabata, inda ya bayyana cewa an zabo Kano ne saboda jiha ta musamman mai dauke dimbin al’umma kwatankwacin wata kasar.

DG na KSACA, Dr. Usman Bashir, ne ya jagoranci tawagar inda ya shaidawa Kwamishinan cewa, an tsara shirin na KP-CARE-2 zai fara aiki a Kano ne a watan Janairun 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending