News
Za Mu Fara Bai Wa Dalibai Rancen Kudin Karatu A Watan Janairu — Shugaba Tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zamanin yajin aiki a bangaren ilimi a kasar nan ya zo karshe yayin da gwamnatinsa za ta fara aiwatar da shirin bai wa dalibai lamunin karatu a watan Janairun 2024.
Bola Ahamad Tinubu bayyana haka ne a wannan Litinin din yayin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na tattalin arzikin Najeriya karo na 29, wanda Kungiyar Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) ta shirya a Otel din Transcorps Hilton, Abuja.
Wani Saurayi Da Budurwa Sun Daurawa Kansu Aure A Jahar Jigawa
Shugaban, wanda ya yi magana game da tsare-tsaren gwamnatinsa na daidaita tattalin arzikin kasar tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, musamman masu zaman kansu, ya jaddada bukatar a gaggauta bullo da shirin ba da lamuni mai dorewa wanda zai taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Jaridar Inda Ranka ta cewa, tun a watan Yunin da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya.
Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi.
Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya.
À wani labarin kuma Wani Saurayi Da Budurwa Sun Daurawa Kansu Aure A Jahar Jigawa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
