Connect with us

News

Fasinjoji 18 sun tsallake rijiya da baya a hanyar Legas zuwa Ibadan

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Akalla mutane 18 ne a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, suka tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya afku a sashin Long Bridge na babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Jaridar The Nationa ta ruwaito cewa, motar bas din Mazda farar da mutum 18 mai lamba FKJ285Y tana jigilar mutane daga Maryland zuwa Ibadan jihar Oyo lokacin da hatsarin ya afku.

Advertisement

Zaben shugaban kasa: Bola Ahmad Tinubu zai san makomarsa ranar Alhamis

Daya daga cikin fasinjojin, mahaifiyar jariri dan wata shida, ta ce: “Ba don Allah da direban ba, da na kasance matattu a yanzu. Mun gode wa Allah da direban da ya ceto.”

Wani fasinja mai suna Abubakar da ke tafiya jihar Kebbi amma ya shirya sauka a Ibadan, ya yi ikirarin cewa kudin da yake da shi ba zai iya kai shi ga jihar Kebbi ba, kuma ya yi kuka yana cewa shi ne ya fi kowa bakin ciki a motar.

Advertisement

Ya ce: “Ni ne wanda ya fi kowa bakin ciki a wannan motar bas, kudin da ke tare da ni ba za su iya kai ni Kebbi ba.

A wani labarin kuma Zaben shugaban kasa: Bola Ahmad Tinubu zai san makomarsa ranar Alhamis

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending