Connect with us

News

Majalisar wakilai ta ƙi yarda a yafe wa ɗalibai kuɗin WAEC da NECO da UTME da JAMB da su rubuta kyauta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

A ranar Laraba ɗin nan ce Majalisar Tarayya ta yi fatali da roƙon neman amincewa da ƙudirin ɗaliban sakandare su rubuta jarawabar NECO, WAEC da JAMB kyauta a zangon 2023/2024.

An nemi a yi wa iyayen yara wannan afuwar biyan kuɗin jarabawar ce saboda a rage masu raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita, tun bayan cire tallafin fetur.

Yan Bindiga Sun Sako Malamar Jam’iar Nasarawa Da Suka Sace

Ɗan Majalisa Anamero Dekeri, ɗan APC daga Jihar Edo ne ys bijiro da roƙon, inda ya roƙi Majalisar Tarayya ta umarci Gwamnatin Tarayya ta biya wa kowane ɗalibi kuɗin jarabawar WAEC, NECO da UTME.

Sai dai kuma an yi fatali da buƙatar Ɗan Majalisar, bayan an yi doguwar mahawara a Zauren Majalisa.

Advertisement

Dekeri ya ce shi dai da zuciya ɗaya ya nemi a yi wa iyayen ɗalibai wannan sassauci, saboda irin halin ƙuncin da suka shiga, tun bayan cire tallafin fetur.

 

Ya ce kuɗin da talakawa ke kashewa kan fetur da tsadar zirga-zirga ya na yi wa ɗan abin da suke samu a yau da kullum babban giɓi.

 

Ya ce tunda Gwamnatin Tarayya ta tara rarar ɗimbin kuɗaɗe tun bayan cire tallafin fetur, to kamata ya yi ta yi wa iyayen ɗaliban da ke fita sakandare sassaucin su rubuta jarabawar 2023/2024 kyauta, ba tare da biyan ko sisi ba.

“A kullum tun da aka cire tallafin fetur, gwamnatin tarayya na ajiye tarar naira biliyan 17.2 a kowace rana.”

Advertisement

Kan haka ne ya yi roƙon cewa Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya ya yi shelar yi wa iyayen ɗalibai sassaucin kada su biya kuɗaɗen NECO, WAEC da UTME.

An yi ta ja-in-ja, daga ƙarshe Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajudeen ya bada fili a yi zaɓe, inda waɗanda ba su so a yafe wa iyayen yara kuɗaɗen su ka yi nasara.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending