Connect with us

News

An Harbe Dalibin Jami’ar Benin Har Lahira A Harabar Makaranta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Jama’a sun shiga firgici da razani a jami’ar Benin (UNIBEN) da ke jihar Edo a karshen mako inda wasu da ake zargin mambobin kungiyar asiri ne suka harbe wani dalibin jami’ar da ke matakin aji hudu (500-level) a tsangayar nazarin kimiyyar Phycical.

A wani faifayin bidiyo an ga yadda jami’an tsaron makarantar suka dauki gawar mamacin cikin wata mota kirar Hilux bayan da maharan suka aikata danyen aikin nasu.

Advertisement

Shugaban ma’aikatan jihar Kano Alhaji Usman Bala ya yi murabus daga mukaminsa.

Jaridar punch ta rawaito cewa Lamarin ya jefa fargaba a zukatan jama’an da suke cikin makarantar da ma yankin, yayin da kuma dalibai da ma’aikata ciki har da malamai hadi da maziyarta suka yi ta gudun neman tsira a lokacin da suka ji karar harbe-harbe.

An nakalto kuma cewa wannan mummunar lamarin bai rasa nasaba da harkokin kungiyar asiri.

Advertisement

An kuma ce, an ajiye gawar mamacin a wani wajen adana gawarwakin da ba bayyana sunansa ba.

Har zuwa lokacin da wakilin majiyarmu ke kammala hada wannan rahoton a yammacin ranar Asabar, hukumomin jami’ar ba su ce uffan kan lamarin da ya farun ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending