Connect with us

News

Tinubu Na Shirin Balaguro Zuwa Kasar Saudiyya

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Shugaba Bola Tinubu na shirin halartar taron kasashen Larabawa da Afirka da Saudiyya da za a yi a makon nan a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Advertisement

Mai bada shawara ga shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a karshen mako yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi ga ma’aikatan kananan hukumomi kan rashin zuwa aiki.

Ya ce halartar shugaban kasar zuwa taron na cikin yunkurin gwamnati na amfani da dukkan hanyoyin da za a jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye daga kasashen waje zuwa sassa daban-daban na tattalin arziki.

Advertisement

Ngelale ya ce za a yi cikakken bayani a taruka daban-daban da shugaban zai yi da masu zuba jari, wadanda suka shafi farfado da tattalin arzikin kasa.

A wani labarin kuma Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi ga ma’aikatan kananan hukumomi kan rashin zuwa aiki.

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending