News
Ƙidaya: Majalisa Wakilai za ta binciki yadda aka kashe Naira Biliyan 200
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Majalisar Wakilai ta ce za ta binciki Naira biliyan 200 da aka kashe kan ƙidayar da aka ɗage a shekarar 2023 da Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa NPC ta yi.
Ƙudurin binciken yadda NPC ta kashe ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da ɗan majalisa Dominic Okafor (APGA- Anambra) da ɗan majalisar wakilai Patrick Umoh (APC-Akwa Ibom) suka ɗauki nauyi a zauren majalisar ranar Laraba.
Ba Zamu Maimata Kuskuren Biyan Jami’nmu Ba A Wannan Karon-INEC
Okafor, wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce “ƙidayar jama’a ta samar da sahihin bayanan yawan jama’a yana da amfani ga tsare-tsaren ci gaba, tsara manufofi, rabon albarkatu, da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.
Ya ce ƙidayar ta fi zama dole musamman a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya tare da gwamnatocin jihohi ke ƙoƙarin bai wa ‘yan ƙasa agajin gaggawa da kuma tsara wasu ayyukan jin daɗin jama’a.
Ɗan majalisar ya ce, NPC tana da hurumin gudanar da binciken ƙidayar lokaci-lokaci, da sauran hanyoyin ƙirga yawan al’ummar ƙasar da kuma samar da bayanan tsare-tsare da ci gaban tattalin arzikin ƙasar.
Okafor ya tuna cewa a shekarar 2006 ne aka gudanar da ƙidayar jama’a ta ƙasa a Nijeriya a shekarar 2023 kuma hukumar ta ɗage ƙidayar 2023 da aka shirya yi a watan Mayun 2023.
A cewarsa, bayanan da aka tattara a ƙidayar shekarar 2006 sun yi nisa daga gaskiya a yau kuma ba za su iya kafa ƙwaƙƙwaran tushe na kafa manufofin tattalin arzikin ƙasa da za su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen gudanar da tsare-tsare masu inganci na ƙasa ba.
Hukumar ta amince da kashe Naira biliyan 200 daga cikin Naira biliyan 800 da aka kasaftawa wajen tsara yadda za a aiwatar da ƙidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023, wanda aka dage.
Idan aka kasa gudanar da ƙidayar yawan jama’a da gidaje a cikin watanni 12, bayanan da aka tattara a duk faɗin ƙasar za su zama almubazzaranci da albarkatun ƙasa, kuma ƙasar za ta kara kashe kuɗi wajen tattara sabbin bayanai in ji shi.
Ya ce Shugaban Hukumar Nasir Kwarra ya bayyana aniyarsa na gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje a ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu a ranar 6 ga Yuli, 2023.
A hukuncin da ya yanke, shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, ya umurci kwamitin kula da yawan jama’a da ya binciki kuɗaɗen da aka kashe kan ƙidayar jama’a da aka ɗage a shekarar 2023.
