News
Yau Litinin 6/11/2023 Kotu za Ta Fara Zama Akan Shari’ar Abba Da Gawuna
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Akwai fargaba a jihar Kano yayin da kotunan daukaka kara ke shirin sauraron karar da Abba Yusuf ya shigar yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta tube shi daga mukamin gwamna.
Kotun, a sanarwar da Sunday Vanguard ta gani, ta nuna cewa za a saurari karar mai lamba CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 a gobe a kotun daukaka kara da ke Abuja.
Ƙidaya: Majalisa Wakilai za ta binciki yadda aka kashe Naira Biliyan 200
Jam’iyyun da ke cikin karar sun hada da Yusuf, jam’iyyarsa, New Nigeria Peoples Party, NNPP, All Progressives Congress, APC, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.
Ku tuna cewa kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Kotun ta soke zaben Abba inda ta bayyana cewa kuri’u 165,663 na sa ba su da inganci, inda ta ce ba INEC ta sanya wa hannu ko tambari ba.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.
Sai dai bayan da kotun ta cire kuri’u 165,663 daga maki Yusuf, an rage masa kuri’u zuwa 853, 939, wanda ya haura kuri’u 30,000 kasa da kuri’u 890,705 da Gawuna ya samu.
A wani labarin kuma Ƙidaya: Majalisa Wakilai za ta binciki yadda aka kashe Naira Biliyan 200
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
