Connect with us

Sports

Ɗan wasan baya na Portugal Pepe ya kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai

Published

on

Ɗan wasan baya na Portugal Pepe

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Ɗan wasan baya na Portugal Pepe ya zama ɗan wasa mafi yawan shekaru da ya zura ƙwallo a raga a tarihin gasar zakarun Turai, inda ya ci kwallon da ta taimaka wa FC Porto ta doke Royal Antwerp.

Pepe mai shekaru 40 da kwana 254 da haihuwa, ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Antwerp a minti na 91, inda ya zama ɗan wasa na farko da ya haura 40 da ya zura ƙwallo a gasar.

Advertisement

Kungiyar Hamas ta lalata motoci 160 na sojojin Isra’ila

 

Francesco Totti ke riƙe da tarihin mai mafi yawan shekaru da ya zura ƙwalo a shekara 38 da kwanaki 59.

Advertisement

 

Pepe kuma shi ne ɗan wasa mafi shekaru da ba mai tsaron gida ba da ya buga wasa a tarihin gasar.

Advertisement

Ya kafa wannan tarihin ne a lokacin da ya fara karawar FC Porto da Antwerp a ranar 25 ga Oktoba.

Mai tsaron gida Marco Ballotta shi ne ɗan wasa mafi yawan shekaru a gasar Zakarun Turai, yana da shekaru 43 da kwanaki 252 da haihuwa a lokacin da ya buga wa Lazio wasa da Real Madrid a watan Disamban 2007.

Advertisement

A wani labarin kuma Kungiyar Hamas ta lalata motoci 160 na sojojin Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending