News
Kotu ta tsare tsohon gwamnan CBN, Emefiele a gidan yarin Kuje
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin a tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele a gidan yarin Kuje har sai an kammala tantance bukatarsa ta neman beli.
Emefiele zai ci gaba da zama a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba, inda kotu za ta yanke hukunci kan bukatar belinsa.
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 6, sun kwato kakin Sojoji guda 40 a Kaduna
Lauyan sa, Mathew Burkaa SAN, ya gabatar da bukatar neman belin wanda Rotimi Oyedepo ya yi kakkausar suka a madadin gwamnatin tarayya.
Alkalin ya ce yana bukatar lokaci kadan don yin nazari a kan hukumomi da kuma duba abubuwan baje kolin da Emefiele ya kawo domin tallafawa bukatarsa ta neman beli.
Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, an tuntubi jami’an hukumar gidan yarin na Kuje da su kawo abin hawa domin kai shi gidan yari.
A wani labarin kuma Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 6, sun kwato kakin Sojoji guda 40 a Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan bindiga shida da suka addabi mazauna karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Wata sanarwa da mukaddashin daraktan yaɗa labaru na sojojin Najeriya, Kanar Musa Yahaya ya fitar, ta ce sun kai samamen ne a ranar Alhamis bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar ƴan bindigar a garuruwan Sabon Birni, Dogon Dawa, Saulawa, da Maidaro- Ngede Allah, da kuma Kidenda duka da ke karamar hukumar Birnin-Gwari
Ya ce dakarun sun yi ba-ta-kashi da ƴan bindigar da fafatawa ta lokaci, inda suka samu nasarar kashe shida daga cikinsu.
A cewar mai magana da yawun sojojin, ya ce sun kuma ƙwato bindigar AK-47 guda biyu, da alburusai goma sha huɗu, da rigunan kaki na ƴan bindigan guda 40, da kuma babura tara.
