Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kirkiro Hukumar Kula Da Filaye

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙudirinta na kirkiro Hukumar Kula da Filaye ta Kasa.

Ministan Gidaje da Tsara Birane, Ahmed Dangari ne ya bayyana hakan, a taron zuba jari na ’yan Nijeriya mazauna kasashen ketare, karo na 6 da ya gudana a Abuja.

Yan Sandan Jihar Gombe sun kama wata mata bisa zargin ta da kashe mijinta ta  da tabarya.

Ministan ya ce samar da sabuwar hukumar zai taimaka wajen kula da hakkin mallakar filaye a kasar nan.

Dangari ya kuma ce kirkiro hukumar na daga cikin sabbin manufofin Gwamnatin Tinubu na saita hanyoyin mallakar filaye.

Advertisement

“Rahoton kwamitin da shugaban kasa ya kafa kwanakin baya ya samar, kan sabbin dokokin mallakar filaye, karkashin Farfesa Peter Adeniyi, za a yi amfani da shi a sabuwar hukumar.

“Babu wata kasa da za ta samu ci gaba, ba tare da ta inganta dokokin kula da filayenta ba, ”in ji Dangari.

A wani labarin kuma Yan Sandan Jihar Gombe sun kama wata mata bisa zargin ta da kashe mijinta ta  da tabarya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya fitar da wasu hotuna da ke nuna jerin gwanon Falasɗinawa na barin Asibitin Al-Shifa a ƙafa.

Rahotonni sun ce ɗaruruwan mutane ne suka fice daga asibitin, wanda dakarun Isra’ila suka mamaye tsawon kwanaki.

Hotunan sun nuna maza, da mata, da yara na tafiya a kan titin da ɓaraguzai suka shafe yayin da wata motar rusau ta sojoji ke wucewa a bayansu.

Advertisement

Wakilin AFP ya ce daga cikin mutanen akwai marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni yayin da suka kama hanyar zuwa kudancin Birnin Gaza daga arewaci.

Tun da fari, ma’aikatar lafiyar Gaza ta ce akwai marasa lafiya 120 da kuma wasu jarirai bakwaini da ba a san adadinsu ba da suka rage a asibitin.

Shugaban asibitin ya zargi Isra’ila da tilasta kwashe marasa lafiyar, amma dakarun sojan ƙasar na cewa wai sun taimaka ne wajen biyan buƙatar da shugaban ya nema.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending